Mulkin mace a mahangar islam

Asslamu alaikum.
Zance mafi inganci kan shugabancin mace a musulunci .

Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da aminci su tabbata ga shubanmu Muhammad da alayensa da sahabbansa, damu gaba daya.
Amma bayan haka:

Lokaci yayi – a ganina – da ya kamata in fadakar da yan’uwa kan  mas’alar nan da ake ta cece-kuce kanta, wato mas’alar shugabancin mace a musulunci .wato ya hallatta mace tayi shugabanci kan mutane a musulunce ko kuwa ?

A dan karamin bincike da nayi – a gurguje -kan wannan mas’alar, na fahimci maluma sun kasu kashi biyu, masu halatta haka, da masu haramta hakan.

Sudai masu haramta hakan suna dogarone da wani hadisi da Imam Bukhari ya ruwaito mai lamba 7099, daga Abi Bakrah, inda yake cewa : manzon Allah yace: لَنْ يُفْلِحَ قَوْمٌ وَلَّوْا أَمْرَهُمْ امْرَأَةً
Ma’ana: Duk mutanen da suka baiwa mace mulki akansu bazasu ci nasara ba.
Su kuwa masu halatta hakan, cewa suke, ai wannan maganar labarine irin na annabta da manzon Allah ke badawa, ba hukunci bane balle a fake dashi a haramta mulkin mace. Dun haka a fahimtar wadannan maluman, Annabi yana maganane da mutanen kasar Farisa, dumin ai tarihi ya nuna cewa, manzon Allah S.A.W. ya taba turawa sarkinsu ( Farisa )  mai suna Hiraqlu da wasika yana kiransa ga musulunci, sai ya yaga wasikar kafinma ya karanta, dun kadama yaji abinda manzon Allah yake fada aciki. Ko da labari ya isowa manzon Allah kan abinda sarkin yayi da wasikarsa,  nan take ya daga hannuwansa masu daraja sama, ya roki Allah da ya yaga mulkinsa shima kamar yadda ya yaga wasikarsa. Addu’ar manzon Allah kuwa ta karbu, dumin dansa Shirawaihi (شيرويه) ya kasheshi, yayi masa juyin mulki.
Shi yasa, lokacinda mutanen Farisan suka zo gun manzon Allah, sai ya tambayesu, wanene kuma yanzu shugabanku ?sai sukace masa wata matace . Sai Annabi yace musu ; ai wadanda suka dora mace akan mulki, baza suyi nasara ba .

Hujjarsu ta biyu kan wannan mas’alar kuwa itace, ai an sami mata da dama bayan fadin haka da Annabi yayi, sunyi shugabanci, kuma anyi nasara. Da kuwa wannan maganar haka take kamar yadda wassu ke fassarawa, da ba’a sami haka ba. Dun fadin manzon Allah baya faduwa kasa. Dun haka a fahimtarsu wannan maganar labarine na annabta da Annabi ya fadi kan mutanen Farisa.Duk da cewa, Kalmar rabauta, tana iya daukar ma’anoni da dama, basai cimma nasara a mulki kadai ba.
Wannan shine a takaice hujjar masu haramtawa da kuma hujjar masu halattarwa a takaice. Dun haka wannan mas’alar, mas’alace ta sabani tsakanin maluma,ba mas’ala bace ta zargin juna, ko kafirta juna ba. Dumin kowa nada fahimtarsa kan hadisin.
To, ammani abinda nake son in yi dan tsokaci kansa dangane da wannan mas’alar ayau shine:

1. Yana da kyau mu kara komawa baya, mu kara karanta wannan hadisin da kyau, da kyakkyawar niya, dun mu fahimceshi yadda ya kamata.

2. Yana da kyau mu fahimci me ake nufi da Kalmar Daula, kuma menene banbancin mulkin daula da mulkin kasa ko jiha, ko gunduma ?

3. Yaya tsarin mulkin mutanen Farisa yake a waccan lokacin, idan mun kwatanta da namu tsarin mulkin ?
Idan dai muna bukatar fahimtar wannan mas’alar hakikanin fahimta, ya zamo dole mu amsa wadannan tambayoyin. Dumin sanin kowani malamine – idan dai kwararre ne a fannin malanta da amsa fatawa – cewar fatawa takan canza gwargwadon canjin yanayi, ko wuri, ko hali. Wato abinda maluman sanin shara’a suke cewa :الفتوى تتغير بتغير الحال والزمان والمكان .
Ma’ana: Fatawa takan canza gwargwadon canjin hali, ko zamani, ko wuri . Dun hakama Allah yake fadi cikin suratul an’ami, aya ta 119 :وقَدْ فصَّل لَكُمْ ماحَرَّمَ عليْكُم إلا ما اضْطررْتُمْ إليْهِ
Ma’ana : Hakika ( Allah ) yayi muku bayanin ( duk abubuwanda ) ya haramta muku, ( dun haka kada ku aikata ) saidai abinda kuka tadda kanku cikin matsi, ( to wannan kuna iya yinsa ).
Amma maluma duka sunyi ittifaqi kan cewa, idan uzuri ya gushe, to haramci ya dawo.
Karamin misali kan haka – ga wanda ba malami ba –:

1. Neman mulki ga musulmi haramunne, kuma akul idan ya nema, to ko an bashi Allah bazai taimaka masa ba. Wannan yazo cikin wani hadisi da Imam Bukhari ya ruwaito mai lamba7146, daga Abdurrahaman bin Samura, inda yake cewa: Manzon Allah yace mani : يَا عَبْدَ الرَّحْمَنِ بْنَ سَمُرَةَ لَا تَسْأَلْ الْإِمَارَةَ فَإِنَّكَ إِنْ أُعْطِيتَهَا عَنْ مَسْأَلَةٍ وُكِلْتَ إِلَيْهَا وَإِنْ أُعْطِيتَهَا عَنْ غَيْرِ مَسْأَلَةٍ
أُعِنْتَ عَلَيْهَا
Ma’ana: ya Abdurrahaman, kada ka taba neman mulki, dumin idan har nema kayi aka baka, Allah zai barka da mulkin ( bazai taimaka maka ba ). Amma idan baka akayi ba tare da nema ba, sai Allah ya taimaka maka.
To, a yanzu kana gani sai muce, kada wani musulmi ya nemi mulki, ya jira kawai sai ranar da akace an bashi ? Kaga anan dole fatawa ta canza, dumin canjin yanayi.

To, mu dawo kan amsa tambayoyin nan namu guda uku da muka zaiyana da farko.

1. Hadisin nan da muka gabatar da farko, ko shakka babu hadisine sahihi, to amma yadda wassu maluma ke fassarashi da cewa, haramunne shugabancin mace takowani hali, ta kowani yanayi, agaskiya akwai son zuciya ciki, ko muce akwai tsagoron jahilci.

Dumin duk masana shara’a cikin maluma sun yadda da cewa, mace bata mulkin jama’a idandai ga na miji. Amma tana iya mulki idan babu musulmi a zahiri ko a ma’ana.  Abinda ake nufi da babu musulmi a zahiri, shine, babushi kwata-kwata, abinda ake nufi kuwa da babushi a ma’ana, shine akwaishi, amma bazai iya gwagwarmayar ba, wata kila saboda bashida karfi, ko abinda ma’anar karfi ya kunsa a babin mu’amala. Dumin samun mulki yana zuwane ta hanya daya cikin biyu. Wanda ake badawa, kamar na gado, ko wanda ake gwagwarmaya a nema, kamar na siyasa.
Dun haka idan mace ta tsaya takara, sa’annan ga wani musulmi shima ya tsaya, to anan sai maluma su dubi abinda ake anfani dashi wurin neman mulkin, kamar nauyin abin hannu, ikon gwagwarmaya, jarunta, da kuma zuciya. Dumin wadannan sune sinadaranneman mulki a yau, wadanda anfi tsammanin samun mulki ga maisu.

Dun haka suka zamanto wajibi ga duk wanda zai nemi mulki. Dun haka maluman shara’a sukecewa :ما لا يتم الواجبإلا به فهو واجب , ma’ana : duk abinda wajibi bazai samu ba sai an sameshi, to shima abin ya zamo wajibi. Dumin misalin mutumin da zai sanya kuri’arsa ga wanda bashida wadannan sifofin, kamar mai kai ajiyarsane a bankin da bashida karfin ajiya, yana iya rushewa da amanar ajiya ta mutane a kowani lokaci !!!

Dun hakama Allah yake cewa cikin suratul Qasas, aya ta 26 إِنَّ خَيْرَ مَنِ اسْتَأْجَرْتَ الْقَوِيُّ الْأَمِينُ ma’ana : lallai wanda ya dace ka bashi amanar aikinka, ya zamo mai karfi kuma amintacce . Kaga ai Allah ma, sai da ya fara anbatar karfi kafin ya anbaci amana.
To, amma idan an sami na miji mai karfi, tare da wadancan sifofi da muka zaiyana, to baya halatta a barshi a dauki mace .Amma maganar cewa, zaben mace ta kowace fiska haramunne, ai kusan maganace ta wadanda suka jahilci shara’a. Dumin musulunci baitaba haramta wani abu ba, sai ya bada mafita kan haka, dumin yanayi na iya canzawa a kowani lokaci. Wannanma shi yasa addinin musulunci ya zamo cikekken addini, mai basira da hikima, dumin yakan kula da yanayi wurin tabbatar da hukunci.
Babban misali da zan bada kan haka, shine:

1. Ai sanyawa mutum jinin wani haramunne, amma lokacinda aka sami wani zai halaka dun rashin jinin, sai a halattar da haka, dun yanayi ya canza.

2. Ajiya a bankin ribah haramunne, amma lokacinda kasa ta zamo babu bankin musulunci, sai a halattar da mu’amala da bankin riban.

3. Haramunne likita na miji yayiwa mace jinya, ko ya karba mata haihuwa. To amma idan ya zamo babu likitoci mata wadatattu, sai a halatta hakan, dun yanayi ya canza, dole fatawa ta canza.

4. Ga kuma hadisin da na gabatar maka, wanda ke haramtawa musulmi neman mulki.
To, sai musulmi ayau suce bazasu fito takara ba, dumin Annabi ya hana a nemi mulki ? Idan suka fadi haka, me kake gani zai zamo makomarsu  ayau ?

Dun haka maluman shara’a suke cewa anan, wannan hadisin bazai haramta neman mulki a yauba, dumin idan musulmi basu fita sun nema ba, bazasu taba samu ba, idan kuwa ba dasu ake damawa ba, to rayuwarsu ayau  zata kasance a wulakance, Allah ya tsare .
To, ai anan kaga musulunci ya bada mafita kan abinda ya haramta, saboda cangin yanayi kawai. To ta yaya malami zai fito yana cewa, ai zaben mace haramunne ta kowace fuska, kuma ta kowani yanayi ? Ko yace to ai ga maza  an samu, ba tare da la’akari da yanayinsu ba. Allah ka tsaremu da jahilci da kuma son zuciya, amin.

2. Dangane kuwa da ma’anar mulkin daula, da yazo cikin hadisin, itace, idan ance daula ana nufin gamaiyar kasashe da suka hade karkashin mulkin mutum guda, dun haka, mulkin kasa ko jiha, wani bangarene na mulkin daula. To, kan wani mulki hadisin yake magana ? Babu ko shakka yana maganane kan mulkin daula, dumin a waccan lokacin cewa ake daular farisa.  Dun haka nema wassu maluma kamar su Sheik Ammar cikin littafinsa mai suna حقآئق الإسلام في مواجهةحملات المشككين , da kuma Sheik Dawood abdu rabbu, cikin littafinsa mai suna ألمفصل في الرد على شبهات أعدآء الإسلام , suke ganin cewa, a duk lokacinda da’irar masarauta ta kankanta,ko nau’in mulkin ya banbanta, to hukunci na iya canzawa. Misali kan haka, ai mazhabar malikiya bata yarda a baiwa mace alkalin alkalai na kasa ba, amma ta yarda a bata alkalin yanki, ko lardi kan wani hukunci da aka kebe mata, dumin anan da’irar mulkinta ya kankanta.  Dun haka anfani da wannan hadisin kan haramtawa mace mulkin jiha ta kowace fuska, ta kuma kowani yanayi, lamarine dake bukatar taka-tsantsan ga maluma masu azarbabi, yan bani-na’iya kan  fatawa.

3. Maluman tarihi sun ruwaito cikin littafai da dama, kamar yadda yazo cikin littafin تفسير القطان ,daدلائل النبوة ,  daتاريخ ابن خلدون,da kuma littafinnan mai suna, الدولة الأموية , عواملالإزدهاروتداعيات المنتظم , cewa, tsarin mulkin daular farisa a waccan lokacin tsarine da ake kira da tsarin الإنفرادية , wato mulkin kadaitaka. Wato duk abinda shugaba ke bukata,  alheri ne ko sharri, sai a aiwatar kawai, ba tare da kalubalantarsa ba, kuma babu wani kundi na tsarin mulkin. To kaga kenan akwai banbanci tsakaninsa da mulkin dake da kundinsa, yan majalisarsa, da mashawarta.
Anan ba ina nufin in tsuke fadin hadisin bane, aa, ina dai kokarin in baiyana maka banbancin dake tsakanin mulkinne guda biyu. Dumin sau da dama, akan sami banbancin hukunci, idan aka sami banbancin aiki .

Dauki – alal ga misali – daular mutanen Saba’i, wadda mace ta shugabanta, wadda malaman tarihi ke kiranta da suna Bilkisu, waddakuma  labarinta yazo cikin suratus-saba’i, kama daga aya ta 20 – 44, cikin surar, da daular Firauna, wanda a takaice labarinta yazo cikin suratul Fajri, kama daga aya ta 10 – 14 . Ai Allah bai zargi daular Saba’i ba, duk da cewa macece ke mulkansu. Dumin tanada mashawarta da yan majalisanta, wadanda take shawara dasu idan mai tasowa ta taso. Gama kadan daga yadda take zama da mashawartanta cikin suratus-saba’in, aya ta 32 , lokacinda Annabi Sulaiman ya aika mata da wasika: قَالَتْيَا أَيُّهَا الْمَلَأُ أَفْتُونِي فِي أَمْرِي مَا كُنْتُ قَاطِعَةً أَمْرًا حَتَّى تَشْهَدُونِ
Ma’ana : yaku mutanen fadata, ku bani shawara kan wannan lamarin nawa, dun saninkune, bana yanke hukunci kan kome sai na shawarceku.

Amma a lokacinda Allah yake bada labarin daular Masar karkashin jagorancin Fir’auna, ai zarginsu yayi, tare kuma da nuna mana mummunan karshe da suka yi. Ga abinda yake cewa cikin suratul fajri :وَفِرْعَوْنَ ذِي الْأَوْتَادِ (10) الَّذِينَ طَغَوْا فِي الْبِلَادِ (11) فَأَكْثَرُوا فِيهَا الْفَسَادَ (12) فَصَبَّ عَلَيْهِمْ رَبُّكَ سَوْطَ عَذَابٍ (13) إِنَّ رَبَّكَ لَبِالْمِرْصَادِ (14)
Ma’ana : Ga kuma Fir’auna mai turaku ( dun azabtar da mutane ). Wadanda suka wuce iyaka( wurin mulkan jama’a ) cikin kasashe. Suka yawaita barna cikinta.Sai Ubangijinka ya zuba musu bulalar azaba. Lallai Ubangijinka yana jiran kowa !!!

Duk da cewar daular Masar a waccan lokacin karkashin na mijine, wato Fir’auna, amma da yake yanayin mulkin nashi mulkine na kadaitaka, shi yake zantar da kome yadda yake so, ko alheri ko sharri, sai Allah ya zargi shugabancinsa.

Anan ina bukatar fahimtar da mai karatune, ya fahimci cewa da nayi a baya, idan yanayi  ya canza, ana bukata maluma su dubi irin hukuncin da ya dace su bada, dumin ya zamo daidai da  abinda yazo.
Dun haka babu wata matsala ayau, idan mukace,za’a iya zaben mace tayi mulki, bias dalilai da suka gabata.

Amma mu taru mu rufe ido muki gaskiya, muce haramunne mace tayi mulki ta ko yaya, kuma ta kowace fuska, gaskiya fadin haka ba magana bace da ta dace ta fito daga bakin almajirima, balle kuma ace malami masanin shara’a.

Dun haka, idan akwai musulmi na miji, mai karfi, haziki, jarumi, masanin lamura irin nayau, to baya halatta a zabi mace.

Amma idan ba’a samuba, a zahiri da ma’ana, to ya halatta a zabi mace, saboda yanayi ya kama hakan, kuma mutum koda shi dan hakimin marasa basirane, bai isa yace da mace musulma gwamma kafiri ba. Kamar yadda malami koda shine Bal’amu, ba zaiyi fatawa da haka ba.

Bari in karkare da dan takaitaccen bayani kan wata yar qasida da Allah ya kaddara ta shigo hannuna, ta hannun wani dan’uwa, wacce wassu ke yawo da ita anan garin Jalingo suna kokarin rikitar da hankalin jahilai da wadanda suka renawa wayonsu cikin jama’a.
Na dubi qasidar, bayan na karanta taken da marubucinta yayi mata kamar haka :

HUKUNCIN SHUGABANCIN MACE GA MUSULMI BAKI DAYA. ZUWA GA DUKKAN WANDA WANNAN AL’AMARI YA SHAFA DAGA AL’UMMA.

Sai na fahimci :

1. Abinda marubucin yake bukatar fada daban, abinda ya fada daban. Wata kila dun rashin hujja kan abinda yake son fada. Dumin cewa yayi :

HUKUNCIN SHUGABANCIN MACE GA MUSULMI BAKI DAYA.

To, shugabanci a wani bangare ? A sallah, ko a khalifanci, ko sarautar gargajiya ?kuma a wani yanayi ? ko a wace kasa ?
Dun haka, lokacinda yazo magana kan wanene shugaba, ko menene shugabanci ? Sai ya koma littafai dake magana kan shugabanci a karkashin daular musulunci, ko limanci.

2. Maganar da yake fadi kuwa kan hadisin dake haramtawa mace shuabanci,  ya kasa fahimtar cewa, ai fatawa tana canzawa bisa  cangin yanayi ko hali, kamar yadda muka yi bayani da farko.

3.  Littafai da ya Ambato sunayensu cikin yar qasidar tasa kuwa, duk littafaine na mazhabar malikiya, wadanda suke magana akan ko shugabanci na addini cikin kasa dake bin tafarkin musulunci, ko limanci a sallah.

4. Hujjojin da yake bukatar kawowa cikin qasidar tasa, duka hujjojine da ya dauko cikin mazhaba daya, wadanda sudinma kan shugabancin addini suke magana ciki, a kuma kasa dake bin tafarkin musulunci.

5. Ya kasa yin adalci ga duk wanda zai karanta yar qasidar tasa, dumin ya kasa kawo fatawar wassu maluma daban kan mas’alar shugabancin mace, bai kuma kawo maganganun maluma kan yadda fatawa take canzawa a shara’a ba. Koda shike yin haka sai kwarerren malami mai adalci.

6. Ya kasa fahimtar cewa, mu muna maganane kan shugabancin musulmi ayau, a kuma wannan kasa, dun kulawa da maslahar musulmine, da kuma karesu daga dukkan sharri. Ba magana muke kan shugabanci irin na khalifanci ba, dun ba shara’a da Alqur’ani ake a kasarmu ba.

7. Ya dimauce har ya kasa fahimtar wai akanme yake magana ?  Shugabanci da tsari irin na nijeriya ne, ko shugabanci da tsari irin na musulunci ?  Dun haka yake fadi cikin yar qasidar tasa shafi na 2 cewa :
……… yazo a cikin littafin Albaharul raiqi, sharhin kanzu daqaiq, shi ko raddul Muhktar juz’I na 4, shafi na 203, cewa yayi ; shugabanci ne gaba daya cikin addini da duniya a matsayin khalifa daga Annabi.

To, da wannan na fahimci bai kamata in tsawaita maida martini kan wannan yar qasidar ba. Dumin marubucinta ya tasamma dimaucewa, tunda ya kasa sanin akanme yake magana ? Mulki irin na khalifanci, ko takara irinta siyasar Nijeriya.
8. Ya kama kansa da kansa, inda yake magana kan hikimar jibintar shugabanci, a shafi na 2, cikin qasidar :

‘’Babbar manufar jibintar shugabanci, kamar yadda malaman musulunci suka ambata shine, shugabanci irin na Annabi cikin tsaron addini da siyasa, duniya da addini.’’  Kamar yadda yazo cikin littafin Ahkamul sultaniyya, shafi na 17.
Anan ko jahilin jahilai yana iya fahimtar cewa, ai maganace wannan akan sharudan manufar shugabanci a musulunce. Ba magana yake kan idan musulmi sun samu kansu cikin rintsi, kamar yadda muka sami kanmu anan jahar, yaya zamu yi  ba.

Wani abinda nake tsammani marubucin ya gafala, ko ince ya jahilta, shine. Idan so samune, musulunci ya mulki musulmi, amma idan haka bai yiwu ba, to a sami musulmi ko yaya yake, dun yafi wanda ba musulmi ba. Dumin kada marubucin ya sake irin wannan kwambalen nan gaba, ina bashi shawara ya dubi littafin حلية طالب العلم ,, wanda Sheik Muhammad Salihul- Uthaimin ya rubuta, akwai bayani dalla-dalla kan  mas’alar da malaman shara’a suke kira تخفيف الشر .

Dun haka wannan yar qasidar bai kamata ace ta dimautar da jama’a ba, dumin abinda take maganakansa dabam, abinda mu kuma muke ciki dabam.
Anan kuma naga ya dace in takaita, sai kuma gaba idan munasabar zance ta kama. Allah ya taimake mu.

Allah muna rokonka, ka kara mana fahimtar gaskiya, ka kuma bamu damar aiki da ita. Ka kuma karemu daga sharrin bin son zuciya, da anfani da addini dun samun abin duniya.
Wannan mas’alar – ya yan’uwa – mas’alace mai saukin fahimta, to amma dashike akwai gurbatattu, masu anfani da sunan malanta, masu mummunar manufa cikin lamarin, shi yasa jama’a suke bukatar dimaucewa. To, ina anfani da wannan damar, dun in jawo hankalin yan’uwa, da muyi hattara da ire-iren wadannan maluman. Mu kuma yiwa kanmu qiyamullaili tun lokaci bai kore mana.Allah ya rufa mana asiri.

Ya Allah muna rokonka, ka kare mana zuciyarmu daga munafurci, ka kare mana harshenmu daga karya da yaudara, ka kuma sanya mana son lahira yafi son abin duniya a rayuwarmu, ka kuma kare mana imaninmu da addininmu.

Daga bisani, ina rokon alfarma ga duk wanda ya karanta wannan Qasidar tawa, da ya kara yadata, dumin a gaskiya akwai masu ci da addini ko malanta  dake yawo suna  rikita yan’uwa kan wannan mas’ala mai saukin fahimta, dun dan abin duniyar da zasu samu.  Allah ya karemu daga sharrinsu, amin.
Naku :

Muhammad Muktar Muhammad Bali
Darul – hadith Jalingo.
Mun gode.Asslamu alaikum.

Malam Muhammad Muktar Muhammad Bali
Darul – hadith Jalingo.
Mun gode.

Comments

Popular posts from this blog

AMCON SET TO TAKE OVER BEN BRUCE COMPANIES

Don't Link Me To Arrested Kidnappers- Chief of Gassol

Governor Yahaya gifts N2m, car to Gombe man who trekked for Buhari